Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Da Kokarin Jami’an Tsaro

0
362

Rabo Haladu Daga Kaduna

BIYO bayan samun zaman lafiya da tsaro a jihar Kaduna , gwamnatin jihar ta yaba da kokarin daukacin jami’an tsaron da suke aiki a jihar, wajen taimaka wa kokarinta na samar da tsaro da zaman lafiya a fadin jihar.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin kwamishinan ma’aikatan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, a wani taron zaman lafiya da aka gudanar a karamar hukumar Kafanchan.

Samuel Aruwan, ya ce bisa kokarin da jami’an tsaron jihar suke yi na tabbatar da tsaro a sassa daban -daban a fadin jihar hakan ta sanya gwamnati ta jinjina musu wanda a yanzu jihar Kaduna ta yi tsaf an samu raguwar ayyukan rashin zaman lafiya .

Kwamishinan ya kara da cewa gwamnati jihar Kaduna ta himmatu wajen ganin an samu zaman lafiya da tsaro a daukacin jihar. Akan hakan ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa gwamnatin jihar goyon bayan da ya kamata wajen ganin sun taimaka wa kokarin gwamnatin jihar na samar da zaman lafiya a fadin jihar baki daya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here