Ma’aikatan Gidan Rediyon Da Talabijin Na Atiku Sun Koka Kan Biyansu Albashi

0
375

Daga Usman Nasidi.

MA’AIKATAN gidan Rediyo da Talabijin na tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, GOTEL, sun koka kan rashin biyansu albashi tun watan Satumban 2019.

Gotel ne kamfanin Atiku mafi girma cikin kamfanonin da ya mallaka.

Bayan kamfanin Gotel, Atiku ne mamallakin kamfanin ruwan gora Faro da lemu Adama Beverages, jami’ar Amurka ABTI da kuma masana’antar sarrafa shinkafa, Rico Gado.

Kafin watan Satumba, ma’aikatan sun koka kan rashin biyansu albashin watannin Yuli, Agusta da Satumba.

Ma’aikatan kamfanin sun bayyanawa manema labarai cewa, bayan sallamar kimanin rabin ma’aikatan kamfanin a shekarar 2016 da Najeriya ta shiga matsin tattalin arziki, ba’a taba karawa sauran ma’aikatan albashi.

“Ma’aikata basu san halin da suke ciki ba.Bamu san lokacin da za’a biya albashi ba. Ma’aikatan Gotel na bin bashin albashin watan Oktoba, Nuwamba, da Disamba.”

Yayinda aka tuntubi, Paul Ibe, mai magana da yawun Atiku Abubakar, ya ce ba zai iya tsokaci kan lamarin ba saboda ya daina aiki a Gotel.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here