OHCSF Ta Canza Wa Manyan Darektoci Wurin Aiki A Gwamnatin Tarayya

0
355

Daga Usman Nasidi.

RAHOTANNI daga wata majiya mai tushe na bayyana cewa an canza wa wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin tarayya wurin aiki a Najeriya.

Wannan sauyi da aka yi ya shafi Darektocin gwamnatin tarayya da ke kan mataki na 15 zuwa 17 a wurin aiki.

Gwamnatin tarayyar kasar ta ba da wannan sanarwa ne a wata sanarwa da aka fitar a karshen makon jiya.

An fahimci cewa gwamnati ta ba wadanda canjin ya shafa lokaci su yi abin da ya dace ko a yi masu ukuba.

Shugaban ma’aikatar gwamnatin tarayya, Folasade Yemi-Esan ta sa hannu a kan wannan takarda.

Yemi-Esan ta zama HCSF bayan Buhari ya sallami Winifred Oyo-Ita
Mukaddashiyar shugabar ma’aikatar ta bukaci Darektocin da aka sauya wa wurin aiki su yi maza su ba da wuri.

Darektoci 36 da ke kan mataki 17 da Mataimakan Darektoci 45 da ke mataki na 16 aka yi wa canjin.

Sauran wadanda za su bar wuraren aikinsu sun hada da Mataimakan Darektoci 26 da ke kan mataki na 15.

Dakta Yemi-Esan ta ba wadanda wannan canji ya shafa daga nan zuwa 30 ga Watan Disamba su bar ofis dinsu.

Tun watan Satumba Dokta Folasade Yemi-Esan ta zama shugabar ma’aikatar gwamnatin tarayya ta rikon kwarya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here