Duk Inda Ba Adalci Ba zaman Lafiya – Ndume

0
308
Mustapha Imrana Abdullahi
DAN majalisar Dattawan Nijeriya mai wakiltar yankin Barno ta Kudu Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa duk inda babu adalci ba za a samu zaman lafiya ba.
Ali Ndume, ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin gidan Talbijin na tashar NTA hausa a shiri mai suna ” A bi Doka”.
Ya ci gaba da cewa sai kowace dan Nijeriya ya tashi tsaye wajen tsare doka da oda sannan a samu ci gaban da ake bukata.
Ya bayar da misali da wasu kasashen Afrika kamar kasar Nijar da ya ce ko kan iyakokinsu ba shinge ake sawa ba a rufe kamar na Nijeriya amma dole in mutum ya je wuce sai ya kare doka ba kamar yadda abin yake a Nijeriya ba.
” ya zama wajibi kowane dan kasa ya bada gudunmwarsa in ana son ci gaba ba tare da samun yayan mowa da na Bora ba, kuma kowa ne mutum a Nijeriya yana da nasa laifin wajen haifar da matsala a kasar don haka kowa ya kalli Kansa domin yin gyara.
Sai dai a tabbatar da cewa matsalar boko Haram in ana son magance ta da zarar gwamnati tana son yin maganin ta za a iya cikin lokaci, ya ci gaba da cewa akwai kananan hukumomi a Jihar Borno da babu mutanen waje a cikinsu kuma babu yan boko haram sai dai sojoji kawai
“Har yanzu jami’an tsaron Nijeriya ba su kai miliyan daya ba a cikin kasa mai kusan mutane miliyan dari biyu, to yaya jami’an tsaron za su yi da aikin da ke gabansu dole sai kowa ya bada tasa gudunmawar in ana son ciyar da kasa gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here