Gwamnati Ta Binciki Kamfanonin Da Suke Yin Takin NPK-Sarkin Noman Bassa  

0
339
Alhaji Ya’u Bala Jingir

Isah  Ahmed Daga Jos

SARKIN noman Bassa kuma Garkuwan Hausa/Fulani na yankin Pengana da ke Jihar Filato, Alhaji Ya’u Bala Jingir ya yi kira gwamnatin tarayya, ta binciki kamfanonin da ta baiwa aikin yin takin NPK, a kasar nan kan irin takin NPK, da suke yi. Alhaji Ya’u Bala Jingir ya yi wannan kiran ne, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce kamfanonin da gwamnati ta bai wa dama su rika yin NPK, basa yin mai kyau. Wani takin NPK da wadannan kamfanoni suke yi, idan ka duba za ka ga duk kasa ce a ciki.

Ya ce sakamakon wannan zalunci da wadannan kamfanoni suke yi, manoma da dama suna yin asara saboda amfani da irin wannan taki, a gonakinsu.

Har ila yau ya ce sakamakon wannan matsala manoma suna gujewa irin wannan taki na NPK, da ake hadawa a Najeriya, suna sayen takin NPK da ake shigowa da shi daga waje, da muguwar tsada.

‘’Don haka ya kamata gwamnati ta sanya ido kan wannan al’amari. Ta rika bin wadannan  kamfanoni tana ganin irin takin NPK da suke yi, don magance wannan matsala’’.

Sarkin noman ya yi bayanin cewa matsalolin da manoman kasar nan suke fuskanta, su ne rashin taki da irin shuka  da  magungunan feshi da taraktocin noma da rashin tallafin gwamnati.

Ya ce duk tallafin noman da gwamnati take bayarwa,   baya isa ga manoma na ainihi, yana tsayawa ne ga  manoma na takarda.

‘’Kamar ni din nan a shekara ta 2015 na noma masara buhu 920, a shekara ta 2016 na noma masara buhu 930, a shekara ta 2017 na noma masara  buhu 997, a shekara ta 2018 na noma masara  buhu 966,  a wannan shekara kuma ina sa ran zan noma masara  sama da  buhu 1000. Amma ban taba samun tallafin komai daga gwamnati ba’’.

Ya ce abin da gwamnati ya kamata ta yi, shi ne  ta bi kauyuka ta binciko ainihin manoma, ta rika tallafa masu da taraktocin noma, da taki da irin shuka da magungunan feshi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here