Lokaci Ya Yi Da Shugabanni Za Su Duba Halin Matsin Da Talakawa Suke Ciki-Rebaran Tutu

  0
  265
  Rebaran Haruna Tutu

   Isah Ahmed Daga Jos

  SHUGABAN Cocin Assemblies of God na Gundumar  Saminaka da ke Jihar Kaduna. Kuma wakilin shugaban cocin na kasa,  a  yankin arewa maso yamma, Rebaran Haruna Tutu ya yi kira ga shugabannin kasar nan,  su dubi halin matsin da talakawan kasar nan  suke ciki, domin daukar matakan gyara. Rebaran Haruna Tutu ya yi wannan kiran ne, a lokacin da yake mika sakonsa, na bikin kirsimeti a garin Saminaka.

  Ya ce muna  kira ga shugabanni masu rike da ragamar shugabancin kasar nan,  su lura   lokaci ya yi da za a dubi halin matsin  da jama’ar kasar nan, suke ciki.

  Ya ce a tausaya wa talakawan kasar nan,  kan halin da suke ciki. A yi duk abin da zai taimaka wajen kawo masu sauki, kan halin matsin da suke ciki.

  ‘’Jagoranci mai kyau, shi ne shugabanni  su dubi halin da jama’arsu suke ciki, idan talakawansu suna jin dadi, nan ne za su ji dadin yin mulki. Saboda haka wannan babban nauyi ne, kuma babban hakki ne, da ke kan shugabanni su dubi  halin da jama’arsu suke ciki,  domin daukar matakan gyara’’.

  Rebaran Tutu ya yi bayanin cewa  bikin kirsimetin  da ake yi, ana tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu ne, wanda  ya kawo  zaman lafiya da alheri da ci gaba a duniya.

  Ya ce saboda haka ya kamata dukkan al’umma a rungumi juna kuma a rungumi wannan  zaman lafiya da ya kawo.

  Ya yi kira ga  manoma su kula da kayayyakin amfanin gonar da suka noma. Kada su barnatar su  yi kokari su amfani da kayayyakin amfanin gonar, wajen ciyar da iyalansu tare da  tattalin shirin yin noma, na damina mai zuwa.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here