‘Yan Sanda Sun Kama Wani Magidanci Da Laifin Kashe Matarsa

0
426

Daga Usman Nasidi.

RUNDUNAR ‘yan sandan Najeriya reshen jahar Ogun sun sanar da kama wani magidanci dan shekara 37, Mutiu Sonola a kan lafin lakada ma matarsa, Zainab dan banzan duka da ya yi sanadiyyar mutuwarta har lahira.

Mai magana da yawun ”yan sandan jahar Ogun, Abimbola Oyeyemi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamba, inda yace sun kama Mutiu a ranar Laraba ne bayan mahaifinta ya kai musu rahoton lamarin.

“Mahaifin Zainab ne ya kai rahoto a ofishin Yan sanda na Ibara a kan cewa an kirasa ta wayar salula an bayyana masa cewa diyarsa ta samu sabani da mijinta wanda ya kai ga ya lakada mata dan banzan duka har ta fita hayyacinta.

Ya kara da cewa ba tare da bata lokaci ba ya garzaya gidanta inda ya dauketa ya mikata zuwa babban asibitin Ijaye, inda a can ne likitoci suka tabbatar da mutuwarta.” Inji mai magana da yawun ‘yan sanda.

Jami’in ‘yan sandan yace a lokacin da magidancin ya gano matarsa ta mutu, sai ya ranta ana kare, amma duk da haka ‘yan sanda sun samu nasarar cafko shi daga mabuyarsa, ya kara da cewa binciken farko ya tabbatar da mutumin ya saba jibgar matarsa.

Daga karshe kakakin ya ce tuni sun mika gawar matar zuwa dakin ajiyan gawarwaki domin gudanar da bincike a kan gawarta tare da gano musabbabin mutuwarta.

Hakazalika kwamishinan Yan sandan jahar Ogun, Kenneth Ebrimson ya bayar da umarnin mika Sonola zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar yan sandan jahar domin gudanar da cikakken bincike a kansa tare da gurfanar da shi gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here