Aisha Buhari Ta Raba Kayan Alheri Ga Manyan Asibitoci 4 A Kaduna

0
682

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

UWARGIDAR shugaban kasa, Aisha Buhari Halilu ta yi rabon kayan abinci ga mabukata a wasu manyan asibitoci guda hudu dake fadin jahar Kaduna a matsayin tallafi ta karkashin gidauniyarta, Aisha Buhari Foundation, ABF.

Hadimi na musamman ga uwargidar shugaban kasa, Aliyu Abdullahi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamba a garin Abuja.

Aliyu yace daga cikin asibitocin da suka samu tallafin akwai asibitin St Gerald, asibitin FOMWAN, Barau Dikko da kuma babban asibitin Rigasa.

Da take raba kayan a madadin gidauniyar, hadimar uwargidar shugaban kasa Zainab Ikaz-Kassim ta bayyana cewa manufar raba kayan abincin shi ne domin tallafa ma marasa karfi da gajiyayyu marasa lafiya.

Malama Ikaz ta kara da cewa Aisha Buhari ta dade tana damuwa da duk abin da ya shafi lamarin gajiyayyu musamman mata da kananan yara.

Ita ma a nata jawabin, uwargidar gwamnan jahar Kaduna, Ummi El-rufai, yayin da ta karbar kayan a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, ta yaba da kokarin Aisha Buhari, sa’annan ta bayyana farin cikinta da yadda take damuwa da mawuyacin halin da talakawa ke ciki.

Hakazalika Ummi ta bayyana godiyarta ga Aisha Buhari da ta zabi jahar Kaduna don raba wannan tallafi.

Kwamishiniyar kiwon lafiya ta jahar Kaduna, Amina Mohammed da kanta ta jagoranci zuwa rabon kayayyakin a asibitocin guda hudu, ita ma ta bayana farin cikinta tare da jaddada goyon baya ga duk ayyukan bayar da tallafi daya fito daga wajen Aisha Buhari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here