Jabiru A Hassan, Daga, Kano.
Al’umar garin Katsira da ke mazabar Unguwar Tudu a karamar hukumar Gwarzo sun yi godiya ta musamman ga shugaban karamar hukumar Gwarzo, Injiniya Bashir Abdullahi Kutama bisa sabunta masallacin Juma’a na garin da ya yi.
Wakilin mu wanda ya ziyarci masallacin ya ruwaito cewa an gina masallacin a shekara ta 2012 a karkashin shirn nan na aiyukan mazabu watau ” Constituency Projects” wanda kuma majalisar karamar hukumar Gwarzo ta sabunta domin a sami yin ibada cikin yanayi maikyau.
Malam Adamu Katsira ya shaidawa wakilin namu cewa sunji dadin wannan aiki da ake yi masu, kuma zasu ci gaba da yi wa Injiniya Bashir Kutama da majalisar karamar hukumar Gwarzo saboda aiyukan alheri da take yiwa al’umar yankin batare da nuna gajiyawa ba.
Da yake karin haske kan gyaran masallatai a karamar hukumar Malam Mustapha Umar Tallo Gwarzo yace shugaban karamar hukumar Gwarzo Injiniya Bashir Kutama ya gyara masallatai na Juma’a masu tarin yawa sannan an sabunta na salloli biyar a gurare daban-daban kamar yadda ake gani a fadin yankin.
Sannan ya sanar da cewa karamar hukumar ta Gwarzo bisa jagorancin Bashir Kutama tayi aiyukan raya kasa masu nagarta wadanda suka hada da gyaran hanyoyi da kwalbatoci da kananan gadoji da magudadun ruwa da kuma gyaran makarantu wanda hakan abin alfaharin al’umar karamar hukumar Gwarzo ne.