Jihar Kano Ta Fara Biyan Sabon Karin Albashi

0
582

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN jihar Kano ta fara biyan ma’aikatanta sabon tsarin karin mafi karancin albashin N30,000 a karshen watan Disamba.

Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) sun amince a kan yin karin kaso 23.2% ga ma’aikatan dake mataki na 7, kaso 20% ga ma’aikatan dake mataki na 8 da kuma yin karin kaso 19% ga ma’aikatan da ke mataki na 9.

Tun a ranar 18 ga watan Afrilu, 2019, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar yin karin albashi .

Sai dai, bayan kungiyar NLC ta kammala cimma matsaya da gwamnatin tarayya, rigimar biyan sabon karin mafi karancin albashin ta koma jihohi.

Bayan jerin ganawa a tsakaninsu a kan sabon karin albashin, gwamnonin jihohi sun amince a kan cewa kowacce jiha ta je ta kara adadin da zata iya biya.

Kwamitin da gwamnatin jihar Kano ta kafa a kan karin albashi ya kammala aikinsa tare da cimma matsaya yayin zamansa na ranar 19 ga wata a kan fara biyan sabon karin albashin daga karshen watan Disamba na shekarar 2019.

Bisa sabon tsarin biyan karin albashin, gwamnatin Kano ta amince tare da fara biyan ma’aikatanta karin albashi kamar haka; karin kaso 14% ga ma’aikatan dake kan mataki na 09, karin kaso 11% ga ma’aikatan dake kan mataki na 10, karin kaso 10% ga ma’aikatan dake kan mataki na 12, da karin kaso 9% ga ma’aikatan dake kan mataki na 13.

Sai kuma karin kaso 8% ga ma’aikatan dake kan mataki na 14 da kuma karin kaso 6% ga ma’aikatan dake kan mataki na 15 zuwa 17.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here