Ina Ba Da  Magunguna Ta Dalilin Sana’ar Wasa  Da  Macizai- Idris Bichi

0
544

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

WANI shahararren mai  sana’ar wasa da  macizai da ke garin Bichi ta jihar Kano Idris Bichi  mai Macizai ya ce ta dalilin kama macizai ya sami magunguna iri daban-daban domin  taimaka wa al’uma a duk inda yake, wanda  hakan ta sanya yake kara  shiga cikin duniya domin  gudanar da  wasa da  macizai iri-iri.

Ya yi wannan bayani ne  a zantawarsu da  wakilinmu  yayin da  suka yi kacibis da  juna a kan hanyarsa  ta zuwa garin Lawajar jihar Kogi ranar Lahadin da ta gabata, inda ya sanar da cewa ya je kasashe irin su Kamaru da  jamhuriyar Nijar domin  kama  macizai da  suka gagara, sannan yana hulda  da  al’umomi daban-daban wadanda suka yi fice wajen nasu sana’o in irin  nasa.

Ya ce  a yawon sa na kama  macizai, ya taba gamuwa da  wata mata  cikin wani daji kuma bayan ya gaisheta, sai  ta ba shi wasu  abubuwa da suka shafi magunguna tare da tabbatar masa  da cewa da  ikon Allah zai iya kama macizai komai karfin turjiyar su, wanda  a cewarsa,bayan sun gaisa tà yi masa wannan bayani sai kawai ya ga wata guguwa ta tashi sama kuma har yanzu bai sake jin labarin ta ba.

Daga nan  sai  ya sanar da  cewa yana  aikin kame macizai  bada ingantattun magunguna wadanda suke da  matukar amfani ga al’uma tare da bayyana cewa kofarsa a bude take ga dukkanin masu  son ganawa da shi  musamman idan akwai bukatar a kame macizai a gidaje da makarantu ko ma’aikatun gwamnati sai  a same shi a garin Bichi domin  a shirye yake  ya kame  duk wani maciji da  ya gagara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here