An Cafke Wanda Ya Tsara Fashin Bankin Da ‘Yan Sanda Suka Dakile Abuja

0
302

Daga Usman Nasidi Da Z A Sada

JAMI’AN ‘yan sanda sun kama wani Ernest Ewim mai shekaru 29 a duniya da ake ganin shi ne ya shirya fashin bankin da wasu ‘yan binidiga suka yi yunkurin yi a wani banki da ke Mpape a Abuja amma ba ayi nasara ba.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi yunkurin fashin bankin ne a unguwar Mpape da ke Abuja a ranar Asabar 28 ga watan Disamban 2019.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Abuja, DSP Ajugunri Manzah ya fitar a ranar Alhamis 2 ga watan Janairu ta tabbatar da kama Ewim.

Sanawarwar ta ce: “Sakamakon binciken da ake gudanarwa kan yunkurin fashin bankin da ake yi a Mpape, ‘yan sandan sashi yaki da masu fashi da makami sun kama wani Ernest Ewim dan shekaru 29 da ke cikin gungun ‘yan fashin da ake nema.”

A cewar sanarwar, wanda ake zargin ya taka muhimmiyar rawa a fashin bankin da ‘yan sanda suka dakile kuma jami’an yan sanda sun kama shi ne a mabuyarsa da ke Kamtampe1 a ranar Laraba 1 ga watan Janairu kimanin karfe 4 na yamma.

“A halin yanzu jimlan wadanda aka kama bisa zargi da hannu a fashin ya kai 5 :- Ernest Ewim dan shekaru 29, Larry Ehizo dan shekara 30, Princewill Obinna dan shekara 24, Timothy Joe dan shekara 21 da Elijah David dan shekara 19.”

Sanarwar ta kara da cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin ta na cigaba da kiyaye lafiya da dukiyoyin mazauna Abuja. Za kuma a gurfanar da wadanda ake zargi a kotu indan an kammala bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here