Filin Kungiyar Kwadago Ba Na Sayarwa Ba Ne – ‘Yan Kwadagon Kaduna

0
447
Mustapha Imrana Abdullahi
SHUGABAN kungiyar kwadago reshen Jihar Kaduna Kwamared Ayuba Magaji Suleiman ya bayyana cewa filin kungiyar da ke layin Lafiya ba na sayarwa ba ne.
Shugaban kungiyar kwadagon ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a harabar ofishin da ke Kaduna, bayan sun wayi gari tun da sanyin safiya da zanga- zangar lumana a game da lamarin.
Ya ci gaba da bayanin cewa su a iya saninsu ba su san wani mutum ko kamfani ba in ban da kamfanin Sahel Technical Services Limited, wanda tun farko da shi aka yi yarjejeniya tsakaninsa da kungiyar kwadago, sabanin irin abin da ke faruwa a halin yanzu.
“Mun zo ne domin yin zaman dirshan a wannan wuri saboda namu ne kuma ba na sayarwa ba ne, mun ce a kawo mutane biyar-biyar daga kowane reshen kungiyar kwadago domin yin wannan taro da manema labarai, inda za mu bayyana wa duniya yadda lamarin yake”. Inji kwamared Ayuba na Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here