Jami’an Hukumar Kashe Gobara Ta Kano Sun Tseratar Da Mutane 11

0
311

Daga Usman Nasidi.

HUKUMAR kashe gobara ta jahar Kano ta sanar da tseratar da mutane 11 daga mutuwa a cikin wasu gobara guda 97 da suka auku a cikin shekarar 2019.

Mai magana da yawun hukumar, Saidu Muhammad ne ya bayyana haka inda ya ce sun kubutar da mutane 11 da kadarori na naira miliyan 33 daga gobara 97 da suka faru a shekarar 2019 a Kano.

Malam Sa’idu ya bayyana ma menema labaru hakan ne a Kano a ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu, inda ya ce mutane uku sun mutu a gobara a Kano a shekarar 2019, hakazalika an yi asarar dukiya da ta kai naira miliyan 15.

Ya kara da cewa a shekarar 2019, sun amsa kiraye-kirayen mutane na hakika sau 9, yayin da sun samu kiraye-kirayen karya guda 10. Sa’idu ya bayyana sakaci wajen amfani da tukunyar girka ta iskar gas a matsayin babban abin da ya janyo gobara a Kano a shekarar 2019.

Sauran dalilan da suka haddasa gobara a jahar Kano sun hada da amfani da kayan wuta marasa inganci, amfani da na’urar dafa wuta ‘heater’, da kuma rashin iya janyo wuta zuwa cikin gida.

Daga karshe kakaki Sa’idu ya yi kira ga jama’a da su guji amfani da kayan wuta ta hanyoyin da bai kamata ba, sa’annan ya shawarce su da su daina ajiye man fetir a gidajensu, musamman a lokacin hunturu don magance yiwuwar tashin gobara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here