KUNGIYAR KUTAMA TUKUR TA GUDANAR DA TARONTA NA SHEKARA

0
489
ALHAJI RABIU MUSA GALADIMA
MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga kalaba

A wannan  makon da ya gabata ce kungiyar Kutama Tukur ta gudanar da taron ta da ta saba yi kowace shekara a garin Kutama da ke karamar hukumar Gwarzo jihar Kano .

An shafe shekara tara kenan ana gudanar da irin  wannan taro .Bayan da aka kammala taron wakilinmu ya tuntubi Alhaji Rabi’u Musa Galadima  Galadiman Kutama,   makasudun shirya irin wannan kasaitaccen taro ko wace shekara sai ya ce “ makasudun shirya wannan taro kowace shekara shi ne ‘ya’ya da jikokin marigayi sarkin kutama, Muhammad Tukur da ke gida da waje suzo a hadu a tattauna batutuwa da suka shafi yadda wannan  zuri’a za ta ciyar da garin Kutama gaba da kuma warware mata wasu matsaloli da suke damunta kana kuma wannan taro wata dama ce da take sanya ‘yan uwa na nesa idan sun zo  sukan zo a hadu domin sada zumunci”.inji shi

Shidai wannan taro ana gudanar da hawa kamar na Daba a garin na kutama inda sama da mutum talatin da uku da  aka baiwa mukamai daban-daban na sarauta wasu a gida suke zaune wasu kuma wajen gida ana haduwa a yi zumunci a tattauna mahimman abubuwa da za a duba mainene yake ci wa garin Kutama da masarautar ta tuwo a kwarya domin a magance.

Alhaji Musa Galadima ya yi karin haske dangane da kalubale da masarautar Kutama ke fama da shi ya ci gaba da cewa “kasan kowa ne dan Adam ko gari shi ma yana fama da irin tasa  matsalar to muma garin Kutama da kewaye matsalar da yake fama da ita matsala ce wadda ake fama da ita tun daga mataki na taraiya zuwa jiha amma da yardar Allah muna bakin kokarin mu muga mun magance ta baki daya ko kuma mu kamanta sauran mubarwa Allah ya yi mana jagora”.inji Galadima.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here