Rundunar ‘Yan Sanda Sun Karyata Batun Kai Wa Jirgin Kasa Mai Zuwa Abuja Hari

0
249
Mustapha Imrana Abdullahi
SABANIN irin yadda aka rika yada jita-jitar wai an kai wa Jirgin kasan da ke jigilar jama’a daga Abuja zuwa Kaduna da kuma Kaduna zuwa Abuja hari.
Wannan jita jitar dai an fara yada ta ne a yau Alhamis da safe, inda rundunar ‘yan sandan suka ce labarin ba shi da tushe balantana makama.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kaduna DSP Yakubu Sabo, ya shaida wa manema labarai cewa batun bashi da tushe balanta makama a game da wannan batu na kai wa Jirgin kasa hari.
Inda ya ce hukumar kula da Jiragen kasa ba ta kawo rahoton faruwar wani lamari mai kama da hakan ba ga rundunar.
Lokacin da aka tuntubi hukumar kula da Jirgin kasan sun karyata faruwar lamarin, da suka ce batu ne mara tushe balantana makama”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here