Mustapha Imrana Abdullahi
SANANNEN dan siyasa a tarayyar Nijeriya Injiniya Buba Galadima, ya bayyana cewa yana ganin mutunci da martabar shugaba Muhammadu Buhari.
Sai dai Buba Galadima ya bayyana cewa shi ba shi da ubangida a siyasa domin gashin kansa yake yi a dukkan al’amuran siyasa.
Buba Galadima ya fayyace dukkan wannan bayanan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da kafar yada labarai ta rediyon BBC mai yada shirinsa da harshen Hausa, inda ya tabbatar da cewa ya sha gwagwarmayar siyasa a Nijeriya don haka yana da cikakken tarihi kwarai a harkar.
Ya ci gaba da cewa shi ya kira taron yan siyasa manya manya a gidan Alhaji Bashir Dalhatu da ke Unguwar Kaji a Kaduna domin sanin dan takarar da za a mara wa baya.
Ya kara da cewa ya rike mukamai daban-daban a siyasun da suka rika kafa wa domin samun ci gaba a kasa baki daya
” An kai sunana a gwamnatin Shagari domin a ba ni minista amma aka canza sunana a cikin dare, sai kuma marigayi Abacha a ba ni aiki a gwamnatinsa”.
Buba Galadima ya kara da cewa yana matukar bukatar yin aiki tare da mutanen kirki domin rikon gaskiya da amana.