Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Jajanta Wa Al’umma

0
627
Mustapha Imrana Abdullahi
GWAMNATIN Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’I, ta jajanta tare da mika sakon gaisuwarta ga iyalan mutanen da suka rasa rai ko suka samu raunuka sakamakon hadarin fashewar Tukunyar Iskar Gas da ta faru a sabon Tasha.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun kwamishinan kula da harkokin tsaron cikin gida da al’amuran yau da kullum na cikin gidan Malam Samuel Aruwan.
Lamarin dai ya faru ne a wani wurin gudanar da harkokin kasuwanci a kan titin Kachiya a unguwar sabon Tasha, da ke karamar hukumar Chikun.
 Gwamnatin Jihar Kaduna na jajantawa wadanda suka samu raunuka daban daban sakamakon fashewar tukunyar Gas din.
Gwamnatin ta kuma godewa hukumomin da suka kai agajin gaggawa da suka hada da masu aikin kashe gobara na Jiha da kuma na tarayya da masu aikin bayar da ganin gaggawa. Hakazalika gwamnatin ta mika sakon gaisuwa da Jinjina ga jami’an tsaron da suka tabbatar da tsaro a lokacin da lamarin ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here