An Karrama Babban Editan Gaskiya Ta Fi Kwabo

0
510

Mustapha Imrana Abdullahi

SAKAMAKON irin ayyukan da ya dade yana gudanarwa domin ci gaban kasa a fannin aikin Jarida da rubuce-rubuce ya sa kamfanin Duniyar kwamfuta da suka wallafa wani babban littafi domin sanar da jama’a ilimin na’ura mai kwakwalwa a cikin harshen hausa suka karrama Babban Editan jaridar GTK, Malam Zubairu Abdullahi Sada.

Kamar yadda kamfanin duniyar kwamfuta ya shaida wa duniya cewa sun bayar da wannan lambar ne ga Babban Editan Sheikh Zubairu Sada saboda irin namijin kokarin aikin da yake yi tsawon shekaru

Kadan daga cikin irin aikin da suka bayyana ya hada da wallafa wata mujallar Hausa da bayanin ilimin kwamfuta da harshen Hausa da suka dade suna wallafawa a kamfanin.

Sai kuma shi wannan babban littafin mai dauke da dimbin ilimin kwamfuta da kamafanin ya ce shi ne ya yi aikin dukkan gyare-gyaren da ke ciki ba tare da gajiyawa ba.

An dai gudanar da wannan taron karramawar ne a lokacin da ake kaddamar da littafin da kamfanin ya wallafa a dakin taro na masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here