An Sanya Aikin Gyaran Hanyar Jos Zuwa Kaduna A Kasafin Kudin Bana -Maitala Jingir

0
383
Alhaji Haruna Maitala Jingir.

Isah Ahmed Daga Jos

DAN majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa  da ke Jihar Filato Alhaji Haruna Maitala Jingir,  ya bayyana cewa an sanya aikin gyaran hanyar Jos zuwa Kaduna, a kasafin kudin bana.

Alhaji  Maitala Jingir ya bayyana haka ne, a lokacin da yake jawabi a wajen taron ranar kabilar Jere da aka gudanar a garin Jingir a karshen makon da ya gabata.

Ya ce ganin irin wahalar da matafiya suke sha kan wannan hanya sakamakon lalacewar da ta yi shekara da shekaru, suka tsaya tare da taimakon mataimakin shugaban majalisar wakilai ta tarayya, Alhaji Ahmed Maje da Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong wajen an sanya aikin wannan hanya, a kasafin kudin bana.

Ya ce don haka tuni a sanya aikin gyaran hanyar a kasafin kudin bana. Abin da ya rage yanzu, shi ne za su tsaya wajen ganin an sami kudaden, da za a zo a fara aikin gyaran hanyar.

Ya bai wa al’ummar mazabarsa tabbacin cewa nan ba da dadewa ba, zai bi dukkan al’ummar mazabar ya bayyana masu, irin ayyukan da suka sanya gaba a mazabar.

‘’Dangane da cibiyar koyar da sana’o’i da kungiyar al’ummar kabilar Jere suke son kafawa, don koya wa matasa sana’o’i  zan kasance ina daya daga cikin wadanda za su yi aikin gina wannan cibiya har a kammala aikin.Don haka ina kira ga al’ummar Jere, mu ci gaba da zaman lafiya, kamar yadda aka sanmu domin babu wani ci gaba da za a samu, idan babu zaman lafiya’’.

A nasa jawabin babban bako mai jawabi, kuma malami a kwalejin ilmi ta gwamnatin tarayya da ke garin Panshin, Mista Auwalu Gimi ya yi kira ga ‘yan kabilar ta Jere su yi kokari su rika tallafa wa ‘ya’ya mata, suna tafiya makarantu, maimakon takura masu su yi aure da wuri.

Ya ce babu shakka akwai matsalar rashin  tura ‘ya’ya mata zuwa makarantu, a kabilar ta Jere. Don haka ya ce ya zama wajibi kabilar Jere, su canza wannan hali su rika karfafa wa ‘ya’ya mata gwiwa, suna tura su makarantu domin a sami ci gaba a kabilar, da kasa baki daya.

Shi ma a nasa jawabin Garkuwar al’ummar Hausa-Fulani na yankin Pengana, Alhaji Ya’u Bala Jingir ya bayyana cewa ya kamata a karrama al’ummar yankin  Pengana, kan zaman lafiyar da suke da shi a yankin.

Ya ce suna da kabilu sama da 20, amma duk rikice-rikicen da aka samu a jihar Filato a shekarun baya, ba a taba samun tashin wani hankali  ba a yankin.

Ya ce wannan babban abin ci gaba ne da ya kamata gwamnan jihar Filato Simon Lalong da shugaban kasa Muhammadu Buhari su karrama yankin kan wannan zaman lafiya.

Tun da farko a nasa jawabin shugaban kungiyar al’ummar Jere na kasa Mista Ibrahim Chukuri ya bayyana cewa babban dalilin da ya sanya suke shirya wannan taro, a kowace shekara  shi ne domin su bunkasa al’adunsu na kabilar Jere tare da tattauna matsalolin da suke damunsu domin su, a dauki matakan magance su.

Ya ce ganin cewa gwamnati ba za ta iya samar wa da dukkan matasan da suka kammala makaranta ayyukan yi ba. Ya sanya kungiyar ta yunkuro don gina cibiyar koya wa matasa, sana’o’i domin su sami abin da za su dogara da kan su. Don haka suke rokon a tallafa masu don ganin sun cimma wannan kuduri, da suka sanya a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here