Banbancin Gwamnatin Buhari Da Boko Haram, Tayar Da Bama-Bamai – Matthew Kukah

0
302

Daga Usman Nasidi.

BABBAN faston katolikan jihar Sakkwato, Matthew Kukah, ya ce banbancin dake tsakanin gwamnati da yan Boko Haram wajen kokarin Musuluntar da Najeriya shi ne Bam

Kukah ya bayyana hakan ne ranar Talata yayinda yake jawabi a wani taron Katolika a kasar Ingila.

Rahoton ya kawo cewa Matthew Kukah yana jawabi ne kan kisan mabiya addinin Kirista 10 da ‘yan kungiyar tada kayar bayan ISWAP suka kashe ranar Kirismeti.

Faston ya tuhumci gwamnati da amfani da hanyoyi daban-daban domin cimma manufa daya na Musuluntar da Najeriya kaman Boko Haram.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta yi kasa a gwiwa wajen dakile yan Boko Haram kuma ta baiwa yan ta’addan damar cin karansu ba babbaka kamar yadda sukeyi yanzu.

“Banbanci daya da ke tsakanin gwamnati da Boko Haram shine Boko Haram na amfani da Bam.”

“Suna amfani da akalan mulki wajen karfafa addinin Musulunci, wanda ke kara musu karfin tunanin cewa zasu cimma manufar hakan ta hanyar yaki.”

“”Yadda abubuwa suke yanzu a Najeriya, da alamun babu niyyar kawar da Boko Haram.”

“Sun samar da abubuwan da ke sanya Boko Haram yin abin da suka ga dama.”

“Idan akwai kasan da dukkan matsayi Musulmi ake bai wa, toh ana nuna cewa addinin Musulunci ake kokarin karfafawa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here