Buhari Da Mataimakinsa Da Gwamnoni 36 Su Fito Su Bayyana Wa ‘Yan Nijeriya Abin Da Suka Mallaka __SERAP

0
430

Rabo Haladu Daga Kaduna

KUNGIYAR rajin adalcin da al’amuran mulki SERAP ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo, da Gwamnoni da mataimakansu, su bayyana dukiyar da suka mallaka cikin wa’adin kwana 7.

SERAP ta bukaci bayyanan dukiyar manyan jami’an siyasar ne kamar yadda suka mika bayanan bisa tanadin doka ga hukuma ko kotun da’ar jami’an gwamnati.

Kungiyar ta nemi bayanin bisa dokar nan ta ‘yancin samun labaru ko bayanai daga gwamnati; tana mai cewa rashin bayyana dukiyar a fili ba ya taimakon gaskiya da amana Shugaba Muhammadu Buhari.

Bayan karewar wa’adin, matukar jami’an ba su bayyana dukiyar ta su ba, SERAP ta ce za ta dauki matakin da ya dace don tilasta su, su bayyana dukiyar.

Shugaban wanda ya sha sukar rashin bayyana dukiyarsa a lokacin da ya hau mulki a 2015 ya fito da kanun bayanan dukiyar ta sanarwa daga kakakinsa Malam Garba Shehu.

Ko a wannan karo bayan dawowarsa mulki a 2019, bayanin ya nuna ba wani sauyi da aka samu a dukiyar ta shugaba Buhari don bai bude wasu ma’ajiyu a bankuna ba.

A bayanan da ake da su, mataimakinsa Osinbanjo, ya fi shi yawan kudi.

A kowanne lokaci jami’an labarun shugaba Buhari na nuna tara dukiya ba ta gaban shugaba Buhari.

‘Yan adawa na caccakar shugaban da cewa yana da dabarun boye abin da ya mallaka ko na ‘yan uwa da iyalansa.

Buba Galadima ya fito da wani zargi da ya shafi gidan shugaban duk da dai fadar ta yi watsi da zargin.

Duk da matsin lambar SEPAP ga kotun da’ar ma’aikatan, ta ki bayyana bayanan dukiyar shugaban da sauran jami’an zartarwa da nuna dokar majalisa kai-tsaye ba ta bata dama ba.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here