BUK Ta Karrama Baturiyar Da Ta Kwashe Shekaru 50 Tana Koyar Da Harshen Hausa

0
323

Daga Usman Nasidi.

JAMI’AR Bayero ta Kano ta shirya wani babban taro a kan harshen Hausa domin karrama wata baturiya ‘yar kasar Poland, Farfesa Nina Pawlak da ta kwashe tsawon shekaru 50 tana bincike tare da karantar da harshen Hausa a jami’a.

Rahotanni sun bayyana cewa Pawlak tana koyarwa ne a jami’ar Warsar da ke Poland, kuma ta yaye dalibai a matakin digiri na uku da suka hada da Hafizu Miko Yakasai da Isah Yusuf Chamo, hakazalika ta tantance wani babban Malamin Hausa a BUKM Farfesa Yakubu Magaji Azare.

Cibiyar bincike a kan harsunan Najeriya ta jami’ar Bayero ce ta shirya taron na kwanaki biyu. Da yake kaddamar da taron a ranar Talata, shugaban jami’ar BUK, Farfesa Yahuza Bello ya bayyana Pawlak a matsayin hamshakiyar masaniya, wadda ta sadaukar da rayuwarta ga bincike da karantar da harshen Hausa.

“Ina farin cikin mika godiyar jami’ar BUK gare ki bisa gudunmuwar da ki ka bamu, musamman wajen horas da manyan malamanmu, da kuma alakar da kika kulla tsakaninmu da manyan cibiyoyi da jami’o’i, da kuma littafan da kika  buga, da ma ziyarar da ki ka kawo mana da kuma kyakkyar tarba da kike ba mu idan mun ziyarce ki.

“Ina mika miki godiyar dalibanmu da malamanmu bisa ilimin da ki ba su, sa’annan ina mika godiya a madadin al’ummar Hausa gaba daya bisa gudunmuwar da kike bayarwa wajen ci gaban harshen a duniya.” Inji shi.

A nata jawabin, Farfesa Pawlak ta bayyana cewa ta sadaukar da lokacinta wajen karantar harshen Hausa ne saboda kara fahimtar juna tsakanin kasasheh Afirka da kasashen Nahiyar Turai.

“Idan na yi murabus daga aiki a shekara mai zuwa, zan rubuta kamus na kalmomin Hausa da na harshen Polish domin dalibai masu koyon Hausa a Poland.” Inji ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here