Gwamnatin Kaduna Ta Haramta Sayar Da Gas

0
366

Mustapha Imrana Abdullahi

GWAMNATIN Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’I ta bayyana haramta sayar da Iskar Gas da ake yin amfani da shi domin yin girki ko walda a wuran gidajen zama ko wurare masu hadari.

Gwamnatin ta ce daga rana mai kama ta yau haramun ne a rika yin sana’ar sake dura Iskar Gas a shaguna inda gidajen jama’a suke ko wurare masu hadari.

Gwamnatin ta ci gaba da cewa ta haramta yin hayar shaguna domin sana’ar dura wa jama’a Iskar Gas a duk wurare masu hadari, kuma hanin ya fara aiki ne nan take.

Da wannan hanin an bayar da umarnin cewa dukkan irin shagunan da ake wannan sana’ar ana umarnin su rufe wurare ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnan na Kaduna ya bayyana hakan ne bayan da ya zagaya inda hadarin Gas din ya faru a wata ranar satin da ya gabata.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun kwamishinan kula da tsaro da harkokin cikin gida Malam Samuel Aruwan.

Tuni aka bayar da izini ga ma’aikata da hukumomin gwamnati masu irin wannan aikin na kare afkuwar haka da su tantance iron wadannan wuraren domin su fitar da tsarin canza wa masu sana’ar wurare ba tare da bata lokaci ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here