Hayakin Gawayi Ya Kashe Matasa Biyu Isah Ahmed Daga Jos  

0
414

Daga Isah Ahmad

 

SAKAMAKON matsanancin yanayin sanyi da ake fama da shi a halin yanzu, a garin Jos  babban birnin Jihar Filato, da sauran wasu sassa na kasar nan,wasu matasa  biyu sun rasa rayukansu, sakamakon shakar hayakin gawayi  da suka kunna a dakinsu, don jin dumi a daren ranar Juma’ar da ta gabata, a unguwar Rikkos da ke garin na Jos.

Su dai wadannan matasa Saminu Idris dan shekara 25 da  Idris Dahiru shi ma dan shekara 25, sun kunna gawayin ne a dakinsu, da nufin su ji dumi da misalin karfe 11 na daren ranar ta Juma’a, suka kulle dakin suka kwanta. Ba su tashi ba, sai da gari ya waye da aka ji shiru aka balle dakin, aka samu sun rasu, sakamakon hayakin gawayin da suka shaka.

  • Marigayi Idris Dahiru

Marigayi Saminu Idris

Da yake yi wa wakilinmu karin bayani kan yadda wannan al’amari ya faru, mai gidan da abin ya faru kuma ‘ya’yan daya daga cikin matasan Saminu Idris, mai suna Labiru Idris ya bayyana cewa abin da ya faru, shi ne a ranar Juma’a da misalin karfe 11 na dare, Saminu ya kira shi a waya. Ya ce ya bude masa kofar gida zai dauki kaskonsa, saboda zai kunna gawayi a dakinsa za su ji dumi.

Ya ce nan take ya sa matarsa, ta tashi ta bude kofar gidan ta ba shi kaskon.

Ya ce da gari ya waye ya fito tsakar gida da misalin karfe 6:30 na safe, sai ya ji kauri ya yi yawa a gidan. Sai ya tambayi matarsa mene ne yake kauri? Sai ta ce ita ma tun da ta tashi, take jin wannan kauri. 

Ya ce ya je ya bude dakin da ake dafa abinci, ya duba bai ga abin da yake kauri ba. Sai ya tafi kofar gida, zai bude kofar kenan, sai ya ji kaurin ya yi yawa. Saboda tagar dakin matasan tana kusa da kofar gidan ne, sai ya ja tagar. Sai ya ga hayaki yana fitowa. Sai ya kira sunan kanin nasa sau biyu, amma bai amsa ba. 

‘’Na bude kofar gida na tafi dakin, na girgiza kofar dakin na ji ta a kulle, saboda sun sa sakata ta ciki, sai na je na tashi makwabta muka buge kofar. Sai muka ga hayaki ya turnuke dakin. Na yunkura na shiga, sai na ga hannun kanina ya kandare, babu alamun yana da rai, hankalina ya tashi a lokacin. Shi ne na gangaro zuwa unguwar Gangaren Jos, inda gidan mahaifinmu yake, na gaya masu abin da ya faru.  Shi ne suka gangara zuwa gidan, kafin mu isa makwabtana sun fito da gawarwakinsu, duk sun rasu su biyu’’.

Ya ce a ranar da wannan al’amari ya faru baya iya yin magana, saboda tashin hankali, kan faruwar wannan al’amari. Ya ce amma daga bisani ya mika komai ga Allah, domin shi ne ya kawo wannan al’amari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here