KUNGIYAR KWALLON KAFA TA ENYIMBA TA KORI MAI HORAS DA ITA

  0
  291
  USMAN ABDALLAH ENYIMBA KOCH

  MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba

  KUNGIYAR wasan kwallon kafa ta Enyimba dake garin Aba jihar Abiya ta sallami mai horas da kungiyar Usman Abdalla daga aikin horas da kungiyar wasa. Shugaban kungiyar Felix Anyasi –Agwu ne ya baiyana sanar da korar yau din nan cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ciki hard a wakilin mu na kudanci.

  Felix Anyansi-Agwu,Ya ce ya zame wa kungiyar ta dauki matakin gaggawar korar mai horas da kungiyar sakamakon zargin rashin tabuka wani abun a-zo-a-gani tun daga lokacin da kakar wasa ta bana ta fara “mun lura maimakon kungiyar ta ci gaba ta rika samun nasara a wasanninta sai ma akasin haka aka rika samu”inji shi

  Hukumar gudanarwar kungiyar ta nada  Fatai Osho ya ci gaba da jan ragamar kungiyar Anyasi-Agwu ya kara da cewa hukumar kungiyar kwallon kafar ba ta yi garaje ba wajen sallamar mai horas da kungiyar sai da ta bi mataki a hankali ta yanke shawarar hakan inji shi .Ya ci gaba da cewa “Tun daga lakacin da kakar wasa ta fara mun lura babu wani abin kirki da ya kulla kungiyar babu wani ci gaban ta ta samu .”

  Da ya juya kan ‘yan wasan kungiyar shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta Enyimba Aba ya gargade su da su kara kwazo fiye da wanda suke da shi a yanzu wajen wasa in ba haka  ba kuwa dan wasa ya san inda dare zai masa .Kungiyar ta yi wa Usman Abdallah fatar alheri  a duk inda ya koma .

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here