KUNGIYAR ‘YAN AREWA MAZAUNA KALABA TA YI TARONTA NA SHEKARA

0
427
AMINU BELLO MUHAMMAD SHUGABAN KUNGIYAR AREWA SOLIDARITY

Musa  Muhammad Kutama, Daga Kalaba

KUNGIYAR Arewa solidarity ta mazauna garin Kalaba jihar Kuros Riba ta  gudanar da babban taron ta a wannan mako a Kalaba jihar Kuros Riba

Makasudun yin taron kamar yadda shugaban kungiyar Alhaji Aminu Bello Muhammad ya sanar wa wakilinmu na kudanci cewa, domin ci gaban duk wani dan asalin arewacin Najeriiya mazaunin Kalaba  da kuma taimakon juna ta hanyar sana’arsa ko kuma aikinsa kana kuma bayar da fifiko wajen taimakawa addini da kuma gyaran makabarta.

Alhaji Bello Muhammad ya ci gaba da cewa “ mun fara sayen kayan yin alwala da tabarmi mun fara raba wa masallatai musamman na kusa da mu nan kafin mu fara tafiya sauran masallatai na nesa”.in ji shi.

 

Shugaban kungiyar Arewa Solidarity yaci gaba da cewa ana samun jama’a ‘yan arewa mazauna Kalaba suna kwarara zuwa shiga kungiyar wanda yawan mambobinta ya haura mutum dari da talatin. Kungiyar Arewa Solidarity kungiya ce wadda ba ta gwamnati ba kuma ba ta da alaka da wata kungiyar siyasa a nan kudanci ko a arewaci .

Da yake yin karin haske game da kungiyar shugaban ya ci gaba da cewa “an san ‘yan arewa a duk inda suke suna da kokarin hada kansu da taimakon juna musammman duba da yadda kowa ya zo Kuros Riba daga jihohinsu na asali don haka akwai bukatar a hada kai a taimaki juna

.Wata matsala da shugaban ‘yan arewa ya fada ita babban kalubalensu na yadda za su hada kan jama’a domin a kara fahimtar juna musamman na nesa da suka ji labarin kafa kungiyar Arewa solidarity ta hanyar karo-karo da ‘yan kungiyar ke yi ne kowane lokaci idan sun yi taro ne suke samun kudaden da suke gudanar da daunin kungiyar.

Karshe ya bukaci kowane dan kungiyar da ma wanda bai shigota ba ya zama mai son zaman lafiya da juna ne. Manyan baki da suka albarkaci taron kungiyar akwai sarkin Hausa-fulani na jihar Kuros Riba Alhaji Salisu Abba Lawan Alhaji Wakala Rawaiya jigo a kungiyar da kuma sauran baki da aka gaiyato daga sauran sassa na jiha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here