Rushe Kasuwanni A Zariya, Ya Sanya Wasu ‘Yan Kasuwa A Cikin Damuwa

0
374

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

RUSHE kasuwannin Dan Magaji da Sabon Gari a birnin Zazzau ya jawo wa ‘yan kasuwa da wadanda suka dogara da su tsananin kunci da tashin hankali. Hakan kuwa ya jefa su cikin wani mawuyacin hali, kamar yadda da yawansu suka sanar.

Daruruwan ‘yan kasuwa sun shiga halin kaka-ni-ka-yi da wannan rusau din saboda an bar su babu tsuntsu balle tarko. A halin yanzu suna ta zaman rashin abin yi saboda ba a ba su wasu shagunan ko yankin da za su zuba kayansu don ci gaba da sana’arsu ba.

Majiyarmu, ta samu labarin cewa wasu daga cikin ‘yan kasuwar, sun  yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta dube su tare da kirkiro musu da hanyar da za su kawo karshen wannan halin da suka fada na rashin sana’a.

An gano cewa, tuni ake ta kokarin gyaran kasuwannin, amma ba a mayar da hankali ba har sai zuwa lokacin mulkin tsohon Gwamnan jihar, Alhaji Namadi Sambo.

A wancan lokacin ne, wasu daga cikin kadarorin gine-gine na ‘yan kasuwar sun koma hannun gwamnatin jihar bayan da suka mayar wa da ‘yan kasuwar kudinsu. Gwamnati sai ta damka su hannun karamar hukumar.

Gidajen da ke tsakiyar kasuwa an karbe su a wancan lokacin tare da biyan masu su. Amma daga bisani, gwamnatin karamar hukumar ta sake sayar da wadannan kadarorin ga ‘yan kasuwa. A halin yanzu kuwa da aka fara rusau din, ‘yan kasuwar na ta koke tare da korafin cewa gwamnatin jihar ba ta biya su hakkokinsu na miliyoyin nairori ba.

Wasu daga cikin ‘yan kasuwar da ke koke sun tura kudin siyan shagunan ne ta wani asusu da ba na gwamnati ba. Wasu daga ciki kuwa hannu da hannu suka ba da kudin sayen shagunan, ga shugaban karamar hukumar Sabon Gari na wancan lokacin.

A lokacin da aka sanar da ‘yan kasuwar cewa za a rushe kasuwar da gaggawa,ya bayyana cewa ba su da wata kwakwkwarar shaida a hannu da ke nuna cewa wadannan shagunan mallakinsu ne.

Daya daga cikin mamallakan rukunin shaguna a kasuwar ya ce, “A tunaninku hauka muke da za mu gina shaguna a kasuwa ba tare da wata shaida ba? A lokacin da dan aiken shugaban karamar hukumar ya bukaci in ba da kudina a hannu, ban bada ba. Sai na ce zan zuba a asusun banki.

A halin yanzu da ya musanta hakan, an binciki tarihin shige da ficen kudi na asusun bankinsa kuma an gani. A don haka muke bukatar tallafin hukumar EFCC.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here