Shugaba Buhari Ya Yi Muhimmiyar Ganawa Da Shugaban NNPC

0
283

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya sa-labule a fadar shugaban kasa na Aso Villa da shugaban kamfanin NNPC na kasa.

A ranar Laraba, 8 ga Watan Junairu ne mu ka samu labarin wannan muhimmiyar tattaunawa tsakanin shugaban na NNPC da Buhari.

Majiyarmu , ba ta iya kawo ainihin dalilin wannan haduwa a rahoton da ta fitar a tsakiyar makon nan ba.

An yi wannan zama ne tsakanin shugaban Najeriyar da shugaban kamfanin man kasar a daidai lokacin da farashin danyen mai ya tashi.

Kudin danyen mai ya tashi da 2.4% a kasuwar waje a makon nan

Gangar mai ya kara kudi a kasuwa ne a sakamakon rikicin da ya ke neman barkewa a Yankin Gabas ta tsakiya tsakanin Iran da Amurka.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gangar man fetur ya dada kudi a duniya bayan sojojin Amurka sun hallaka wani babban sojan kasar Iran.

Ta ce shugaba Muhammadu Buhari zai kuma yi wani irin wannan zama anjima da karamin Ministan fetur na Najeriya, Timipre Sylva.

Kudin danyen mai ya yi tashin ta Najeriya ta fara saida ganga guda a kan $70, karon farko da mai ya yi kudi haka tun Watan Yunin 2019.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here