Wata Hatsabibiyar Gobara Ta Kashe Wata Uwa Da ‘Ya’yanta 3

0
378

Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

A rahoton da ya fito daga ma’aikatar kashe gobara a jihar Yobe, ta tabbatar da cewa wata gobara da ta tashi a rukunin gidaje ta Red Bricks ta yi  sanadiyyar mutuwar wata uwa tare da ‘ya’yanta guda uku, a wannan unguwar wadda ke kan titin Damaturu zuwa Maiduguri, da daren ranar Talata.

Da yake tabbatar da abkuwar lamarin, jami’in hukumar kashe gobara, a Damaturu babban birnin jihar, Usman Habu, ya ce gobarar ta tashi ne da kimanin karfe 11:00 na dare. Ya ce “Inda nan take aka sanar da mu abin da ke faruwan; na tashin gobara a rukunin gidaje da ke Red Bricks, kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri”.

“Haka kuma, a lokacin da muka isa wajen, mun fahimci kokarin da mahaifin wadanda gobarar ta rutsa da su, Malam Adamu Aliyu, wajen kokarin ceto iyalin sa amma ina, abin ya faskara, duk da ya yi nasarar ceto ran karamin dansa, dan shekaru biyar, mai suna Faruk Aliyu”.

“Wanda a tashin farko yadda gobarar ta kama ka’in-da-na’in, ya jawo duk iya kokarinsa na kubutar da sauran iyalan abin ya gagara, wanda hakan ya tilasta masa tsallakowa ta kan katanga, don shi ma ya kubuta”.

Babban jami’in hukumar ta kashe gobarar ya kara da cewar,  bayan zuwan jami’an nasa ne aka yi nasarar balle kofar gidan, inda suka tarar da gawar matar tare da sauran gawarwakin ‘ya’yanta guda uku”.

Wata daga cikin makwabtan gidan, Binta Mohammed, ta bayyana matukar alhinin ta dangane da wannan babban rashi na wadannan ‘yan mata; Ai’sha Aliyu, Sa’adatu Aliyu, da Safiya Aliyu. A asibitin kwararru ta Sani Abatcha da ke Damaturu,

Daya daga cikin likitocin asibitin Dokta Istifanus Dauda ya tabbatar da lamarin tare da bayyana cewa, karamin yaron da aka kwantar a asibitin bisa dalilin kunar da ya samu, yana samun kulawar likitoci a asibitin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here