Ya Tunkari Jami’an Tsaron Soja Dalilin Karbar Na-goro

0
285

Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Maiduguri

GWAMNAN  jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da Kwamandan Rundunar Yaki Da Boko Haram, Janar Olusegun Adeniyi, sun yi cacar-baki sakamakon bukatar da jami’an tsaron ke yi wa matafiya su nuna katin dan kasa kafin su shiga Maiduguri ko kuma su biya Naira 500 zuwa 1,000 na haka siddan.

Danagane da hakan ne Gwamna Zulum ya caccaki jami’an tsaron na Nijeriya a cikin kakkausan harshe dangane da yadda suke karbar na goro kusan Naira 500 zuwa Naira 1,000 wajen matafiyan da ba su dauke da katin shaidar dan kasa (National ID Card) kafin su bar su su wuce.

Gwamnan Babagana Zulum ya yi wadannan kalaman ne a lokacin da ya ziyarci babbar hanyar da ta tashi daga birnin Maiduguri zuwa Damaturu sa’ilin da dubban  matafiya suka yi cincirindo bayan da jami’an tsaron suka datse hanyar tare da hana ababen hawa wucewa bisa matsalar hare-haren Boko Haram da ya yi kamari a ’yan kwanakin nan.

Gwamna Zulum, wanda ya yi tattaki har zuwa mashigar birnin Maiduguri daidai shingen binciken ababen hawa yadda ya gana da dandazon matafiyan wadanda suka  yi cirko-cirko a gefen hanya suna jiran jami’an tsaro su bude don shiga birnin na Maiduguri.

Zuwan Gwamnan ke da wuya ya daga murya sama yana cewa, “sam wannan ba zai yiwu ba. Ta yaya za ku rika yi wa jama’a irin wannan gallazawa da sunan katin dan kasa? Sannan kuma kun zo kun tattaru kuna karbar Naira 500 da Naira 1,000 a hannun wadannan matafiya, wadanda talakawa ne, kawai saboda ba su da katin dan kasa!”

A lokacin da sojan da ke bakin aikin ke kokarin yi wa Gwamnan karin bayanin dalilansu, nan take ya katse shi, yana mai cewa, “ba gaskiya ba ne, saboda gwamnatin tarayya ba ta samar da gamsasshen tsarin da zai taimaki ’yan kasa su samu katin dan kasa ba. To, ta wane dalili ne zai sa ku zo nan ku tsaya kuna karbar Naira 500, wasu Naira 1,000, kuna neman abin da kwata-kwata gwamnatin ba ta samar da shi ba?”

Gwamna Zulum ya kara da cewa, ya yi ta samun korafe-korafen jama’a da dama dangane da zargin jami’an tsaro na karbar kudaden katin dan kasa a shingayen binciken ababen hawa da ke birnin Maiduguri.

Bayan da cacar bakin ta yi tsamari tsakanin Gwamnan da wasu jami’an da ke kula da shingayen nan da nan  ya umarci masu taimaka masa su kira masa Kwamandan rundunar sojojin yaki da Boko Haram na Lafiya Dole, Janar Olusegun Adeniyi. ta hanyar wayar tafi-da-gidanka yadda aka  jiyo Gwamnan yana cewa,“Kwamanda ka na ina ? Saboda a halin da ake ciki yanzu Ina tsaye a bakin shingen binciken ababen hawa na daf da jami’ar jihar Borno, inda dubun-dubatar matafiya suka yi cincirindo kuma ana karbar kudade daga gare su, saboda ba su da katin dan kasa. Ko akwai dalilin yin hakan?”

Bayan hakan sai Farfesa Zulum ya bai wa jami’in tsaron da ke wajen umarnin ya bude hanya kowa ya tafi abinsa.

Dangane da hakan ne wasu daga cikin wadannan matafiya sun shaida wa wakilinmu cewa, sun kwashe awanni tsaye a bakin shingen ba tare da wani cikakken bayani ba, inda daya daga cikinsu mai suna Umar Hassan ya kada baki ya ce, “tun misalin karfe 8:00 na safe na bar Damaturu kuma na zo nan kimanin 10:00, amma Ina tsaye a wajen har karfe 3:00 na yamman nan ba tare da na shiga gari ba.”

Haka nan wata mata da ta nemi a sakaya sunanta, wacce ta fito daga Kano zuwa Maiduguri, ta ce, “sun ce sai na ba su Naira 500, saboda ba ni da katin shaidar dan kasa, alhalin ba ni da ko sisin da zan bayar, saboda mun kwana a Damaturu jiya ta dalilin mun zo a makare yayin da kuma sojoji sun hana mu wucewa, domin sun ce karfe 5:00 ta wuce. A haka muka kashe ’yan kudin da ke hannunmu.”

Mista Adeniyi ya zo inda wannan al’amarin ya faru a makare tare da kokarin yin karin haske dangane da yadda aka samu cincirindon jama’a, inda ya ce jami’ansa ba su aikata hakan da gangan a wajen ba.

Ya ce ”wannan ya faru ne, saboda harin da aka kai da safiyar ranar da lamarin ya faru” Sannan kuma ya bayyana cewa rundunarsa za ta gudanar da binciken wadannan zarge-zargen, don samun tabbacin ko gaskiya ne; lamarin da Gwamna Zulum ya kafe kan cewa ba zargi ba ne, gaskiya ce, “saboda ni na gan su da idona suna karbar kudin kuma na tattauna da mutanen da aka ce su bayar da kudin!”

A haka cacar baki ta kaure tsakanin Gwamnan tare da janar din soja, inda kuma aka yi rabuwar da ba a fahimci juna ba a tsakaninsu, wanda daga nan kuma a fusace Gwamna Zulum ya wuce zuwa kauyen Jakana mai tazarar kilo mita 45 daga Maiduguri, inda maharan Boko Haram suka kai hari a ‘yan kwanakin nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here