‘Yan Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga, Sun Kona Tutar Amurka Kan Kisan Soleimani

0
325

Daga Usman Nasidi.

‘YAN kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) wacce aka fi sani da Shi’a a ranar Litinin, 6 ga watan Janairu, ta jagoranci wani tattaki hanyar Banex, yankin Wuse har zuwa shataletalen Burger a babbar birnin tarayya, Abuja.

Mambobin na IMN na zanga-zanga ne a kan kisan babban kwamandan sojin Iran, Qasem Soleimani biyo bayan wani hari da kasar Amurka ta kai kansa a ranar Juma’a da ya gabata.

Mambobin kungiyar na kuma neman a saki shugabansu El-Zakzaky da matarsa, Zeenat wadanda ke tsare a hannun hukumar DSS a jihar Kaduna.

Fusatattun masu zanga-zangan sun fito unguwannin Abuja, suna wakokin sukar gwamnatin Amurka.

Sun kuma kona tutar Amurka sannan sun kasance dauke da allunan sukar kisan babban janar din Iran.

A baya mun ji cewa babban sufetan ‘yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ya umarci jami’an ‘yan sandan Najeriya su zauna a cikin shiri ta yadda komai ta fanjama fanjam.

IG Adamu ya bayar da wannan umarni ne biyo bayan kisan wani babban kwamandan yaki na kasar Iran da gwamnatin kasar Amurka ta kashe shi a makon da ta gabata, inda ya ce sun samu labarin akwai wasu da ke shirin tayar da hankulan jama’a a Najeriya tare da yi wa gwamnatin Najeriya zagon kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here