Zan Kammala Ayyukan Bafarawa Da Wamakko – Tambuwal

0
350

Mustapha Imrana Abdullahi

GWAMNAN Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana aniyarsa ta kammala aikin da gwamnatocin tsofaffin Gwamnoni irin su Bafarawa da Wamakko suka bari ba a kammala ba.

Gwamna Tambuwal ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata lokacin da ya kai ziyarar ganin yadda ake aikin ganin babbar kotun jihar ake ganawa a yankin Isa a karamar hukumar Isa a Jihar Sakkwato.

Gwamnan ya bayyana cewa an fara aikin ne a shekarar 2006, inda ya ce gwamnatisa ta mayar da kammala ayyukan da ta gada daga wadansu gwamnatocin da suka gabata kasancewar an zuba makudan kudade da yawa wajen aiwatar da su.

Ya ci gaba da cewa bayan sun duba baki dayan ayyukan da gwamnatin Bafarawa ta bayar na gina ofisoshin shiyya na babbar kotun jiha a Isa,Gwadabawa  da Tambuwal, gwamnatin da yake yi wa jagorancin ta yanke shawara  kammala su baki daya.

Kamar yadda ya bayyana za a zuba makudan kudin da suka kai miliyan 226 domin kammala ayyukan.  Sai dai Gwamnan ya bayyana farin cikinsa da irin aikin da ake yi mai nagari, ya kara da cewa an yi aikin yi wa babbar kotun jihar Sakkwato kwaskwarima da kudi naira miliyan 525 inda aka daga darajarta.

Tambuwal ya kuma ja hankalin jama’a da cewa wannan aikin kammala baki dayan wadannan ayyukan kada a siyasantar da shi. “Saboda muhimmancin aikin ga rayuwar jama a ya sa gwamnatinsa yin aikin batun wurare lantarki da ke Kalambaina. Aikin ya hada da na gidan Salanke domin samar da gidaje aikin makarantar aikin gona ta Wurno da makarantar koyon aikin shari’a da ke Wamakko,” inji Tambuwal.

Tambuwal ya kara fadakar da jama’a cewa tuni ya kammala aikin samar da ingantaccen ruwan sha na Asari,Gagi, Runjin sambo da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here