Babu Abin Da Ya Kai Ilmi A Duniya- Sheikh Yusuf Sambo

0
817

Isah Ahmed Daga Jos

MATAIMAKIN shugaban majalisar malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Yusuf Muhammad  Sambo Rigachikum ya bayyana cewa babu abin da ya kai ilmi a duniya. Sheikh Yusuf Sambo ya bayyana haka ne, a lokacin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da gidauniyar neman taimakon kudi, naira miliyan 75 don gina makarantar addinin musulunci ta Higher Islamic  a garin Unguwar Bawa, da ke Karamar Hukumar Lere  da sayen motoci da babura da reshen kungiyar na Jihar Kaduna, wanda aka kaddamar.

Sheikh Yusuf Sambo wanda Mataimakin shugaban majalisar malamai na kungiyar reshen Jihar Kaduna,  Ustaz Auwal Sa’eed Jika  ya wakilta ya yi bayanin  cewa, rayuwa ba ta zama ingantatta sai da ilmi. Kuma ba a sanin addini sai da ilmi. Don haka mutane su tashi su yi karatu, domin  shi ne babban jihadi.

Ya ce  mutane  su kula da karatun ‘ya’yansu, su  tallafa wa ‘ya’yan marayu da makwabta  wajen yin karatu.

A nasa jawabin Mainan Zazzau Dokta Muhammad Sani Bello ya yi kira ga al’ummar musulmi su rika tallafawa wajen gina makarantun addinin musulunci, domin ci gaban addinin.

Mainan na Zazzau wanda Alaramma Abdullahi Yakubu ya wakilta, ya yaba wa wannan kungiya kan kokarin da take  yi wajen yada ilmi a kasar nan.

Ya ce  ganin irin kokarin da wannan kungiya take yi wajen yada ilmin addinin musulunci, ya sa a kullum Mainan Zazzau yake da  kudurin ganin ya tallafa mata.

A nasa jawabin Daraktan tsangayar kula da muhalli da makamashi ta Jami’ar Jihar Kaduna, Dokta Yahya Saleh ya yi kira ga musulmi su hada kansu,  su yi taimakekeniya wajen raya addinin musulunci.

Ya ce taimako yana da matukar mahimmanci a addinin musulunci.  Kuma  duk wanda ya taimaka aka gina makaranta, yana da lada mai gudana.

Tun da farko a nasa jawabin, shugaban majalisar malamai na kungiyar reshen Jihar Kaduna Sheikh Muhammad Bello Adam Saminaka, ya bayyana cewa sun shirya wannan taro ne, don neman taimakon samar da fili don gina mazaunin wannan makaranta, na dindin a garin Unguwar Bawa.

Ya ce ya zuwa yanzu wannan makaranta ta fara karantar da dalibai a wani wuri na aro, don haka  take son ta sami nata filin ta gina mazauninta  na dindindin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here