Masari Ya Amince Da Kasafin Kudin Bana

0
380

Mustapha Imrana Abdullahi

A ranar Alhamis  Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya sanya wa kasafin kudin shekarar 2020 hannu, a gidan gwamnati bayan amincewar Majalisar Dokokin Jihar ta yi da kasafin kudin.

Kasafin kudin wanda Gwamna Masari ya gabatar wa Majalisar a cikin watan Nuwanbar 2019, na sama da Naira biliyan 249 majalisar ta rage shi zuwa Naira bilyan 244 bayan tantancewar  da majalisar ta yi.

A  lokacin da yake sanya wa kasafin kudin hannu, Gwamna Masari ya ce, za su tabbatar da cewa sun kammala aiyukan da aka faro ba’a kammala. Kazalika, gwamnati za ta inganta bangaren aiyuka na musamman da sashen kasafin kudin da tsare-tsare ta hanyar yin taro da jama’a yadda za su fahimci muhimmancin shi kasafin kudin da ake yi.

Gwamna Masari, ya ce, “Za mu fara yin wannan taro na dandalin saduwa da jama’a kai tsaye a cikin zango na uku na wannan shekara. Shirin kuma za mu yi shi ne a matakin shiyya wadda za mu karkasa shiyyar zuwa wasu bangarori ta yadda za’a ba jama’a damar sanin abin da ke faruwa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here