‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Makaranta A Kaduna, Sun Sace Dalibai 4

0
412

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WASU ‘yan bindiga a ranar Laraba sun kai hari makarantar katolika da ke garin Kakau, hanyar Abuja zuwa Kaduna kuma sun yi awon gaba da dalibai hudu.

Shugaban makarantar, Joel Usman, ya bayyana cewa harin ya faru ne da misalin karfe 10:30 da 11 na daren Laraba.

Ya ce ” Wasu ‘yan bindiga sun kawo hari makarantar Good Shepherd Major Seminary jiya 8 ga watan Janairu, 2020 tsakanin karfe 10:30 zuwa 11 na dare.”

“Bayan kirga dalibai da jami’an tsaro, mun nemi dalibai hudu mun rasa.”

Amma har yanzu hukumar ‘yan sanda ba su saki jawabi kan lamarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here