Harin Bom Ya Kashe Mutane 35 a Kasuwar Gamboru

0
405
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Maiduguri

WANI harin Bom da wasu maharan da ake kyautata zaton mayakan Boka Haram ne suka kai garin Gamboru da ke kan iyakar Nijeriya da kasar ya yi sanadiyyar haka mutane akalla 35.

Wata majiyar da ke garin na Gamboru ta bayyana cewar, wannan lamari ya faru ne da wajen  misalin karfe 4:00 na yammacin ranar da lamarin ya faru, lokacin akwai cincirindon jama’a, a kan gadar bakin kasuwar garin.
Wani ganau a wurin da bam din ya tarwatse gab fa yana wajen da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidar da cewa tashin bam din ya yi kaca-kaca da jama’ar da lamarin ya rutsa da su a ilahirin bakin gadar, abin babu kyaun gani matuka.
Ya kara da cewa, “Kawai sai karar fashewar wani abu; mai karar gaske a wajen, kafinmu fahimci abin da ke faruwa, wanda da idona na ga bangarorin jikin jama’a zube a kasa, yayin da kananan yara sai kukan neman dauki suke.
Wannan lamari matuka ya girgiza hantar jama’a”,“da hannuna na kirga gawarwakin jama’a kimanin 32 wadanda tashin bam din ya rutsa da su. Kuma abin ya faru ne kan gadar Fotokol wadda take kan iyakar Nijeriya da Kamaru.”
Shi kuwa  wani bawan da shi ma ke harabaar wurin da wannan bom ya tashi Malam Mohammad, wanda ya bayyana cewa har yanzu ba a kammala tantance sanin abin da da  ya haifar da tashin bam din ba.
” Ya kara bayyana cewa, mutane da dama sun samu raunuka, wanda mafi yawansu mata da kananan yara ne. Sannan kuma tashin farko mun kwashe mutane 35 zuwa asibiti.
 Malam Muhammad ya ci gaba da cewa kuma mutane da yawa sun gamu da raunuka. “Wannan babban abin takaici ne wanda ya tayar ma na da hankali tare da nuna matukar damuwa. Saboda ya faru a daidai lokacin da jama’a ke kai komo kan wannan gadar da ta hada kasarmu Nijeriya da Jamhuriyar Kamaru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here