Abin Da Ya Sa Muka Yi Yakin Biyafara – Yakubu Gowon

0
256

Rabo Haladu Da Z A Sada Daga Kaduna

TSOHON shugaban mulkin soja na kasar nan Janar Yakubu Gowon, wanda a karkashinsa ne aka fafata yakin Biyafara, ya ce sun shiga yakin ne “saboda kaunar Najeriya”.

Gowon ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da manema labarai yayin da ake cika shekara 50 da kawo karshen yakin a ranar Laraba.

“Wannan yaki an yi shi ne saboda zaman Najeriya kasa daya, ba kamar yadda wasu suke son ballewa ba,” in ji Gowon.

Ya ci gaba da cewa: “Saboda haka babu abin da zai sa na yi nadamar abin da muka yi domin kuwa kaunar Najeriya ce ta sa muka yi.”

A cewarsa, an kammala yakin “ba wanda ya ci nasara kuma ba wanda ya kasa.”

Tsohon shugaban kasar ya kuma bayyana ra’ayinsa kan masu neman a koma mulkin karba-karba inda ya ce “idan za a iya yin wannan kuma zai kawo zaman lafiya, a yi shi idan ana so.”

Ya kara da cewa akwai lokacin da jam’iyyar PDP ta fara magana kan batun kuma “idan da an ci gaba da wannan watakila kabilar Igbo za su iya daukar mulki a lokacin, to amma wannan bai yiwu ba.”

Ya bayyana rashin damuwarsa kan aiwatar da tsarin na karba-karba “idan za a yi wannan a yanzu” yana mai cewa “kowa ne zai iya mulkin Najeriya.”

“A Najeriya akwai mutane da yawa wadanda idan Ubangiji ya ba su wannan lokaci, idan za su iya yi don tsoron Allah, don kaunar jama’a, Najeriya za ta iya ci gaba yadda ya kamata.”

A karshe tsohon shugaban n Najeriya, Janar Yakubu Gowon ya gode wa Allah kan kawo karshen yakin shekara 50 da suka gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here