Gwamna Buni Ya Kafa Cibiyar Kula Da Kananan Yara

0
287

Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

GWAMNAN jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya aza harsashen gina cibiyar kula da kananan yara (MNCH) wadda aka ware naira biliyan 1.6 wajen gina ta, a babban asibitin koyarwa na jami’ar jihar Yobe, da ke Damaturu babban birnin jihar,.

Wannan cibiya dai za ta taimaka wajen rage mutuwar kananan yara tare da kamuwa da gagararrun manyan cutukan da kan yi lahani ga rayuwarsu, a fadin jihar.

Bayan wannan cibiya kuma, Gwamnan ya kaddamar da raba kekunan daukar majinyata masu tayoyi uku-uku guda 28, wadanda za a rarraba su a bangarorin jihar don aikin jigilar majinyata a lokacin ko-ta-kwana tare da saukaka matsalolin zirga-zirgar majinyata zuwa cibiyoyin kiwon lafiya a birane da yankunan karkara a fadin jihar.

Da yake kaddamar da ayyukan, Gwamna Buni ya nanata cewa gwamnatinsa za ta yi iya matukar hobbasa wajen sake fasalta fannin kiwon lafiya ta hanyar kara bunkasa bangaren kana da fadi- tashin habaka ilimi tare da kwarewar ma’aikatan lafiya da ke aiki a cibiyoyin kiwon lafiya a fadin jihar, musamman babbar asibitin koyarwar jami’ar jihar Yobe, wanda hakan zai bayar da cikakkiyar dama wajen gudanar da aikin cikin tsanaki.

Haka kuma ya ce, ‘’babbar manufarmu a nan ita ce don mu ribanya kokarinmu wajen bunkasa samun koshin lafiyar kananan yaranmu tare da rage matsalolin mutuwar kananan yara da kamuwa da gagararrun cutukan da kan yi lahani ga rayuwarsu a fadin jihar Yobe’’.

Gwamnan ya nanata cewar, ‘’babban burin da gwamnatinmu ta sa a gaba shi ne ci gaba da kyautatuwar fannin kiwon lafiya, kuma abin da muke fadi-tashi a kansa shi ne nemo hanyoyin da za mu kara bunkasa ci gaban asibitin koyarwar jami’ar jihar Yobe hadi da kara horas da ma’aikata tare da kwararrun likiticinmu’’.

A cewarsa ta hakan ne za su kai ga cimma nasarorin da suke hankoron su cimma tare da kasancewa karkashin kulawar yardaddun hukumomin da ke gudanar da su.

Haka nan  kuma, ya ce gwamnatin jihar tana da kudurin ci gaba da daukar karin kwararrun manyan ma’aikata a fannin kiwon lafiya, a bangarorin kiwon lafiya daban-daban, don aiki a babbar asibitin koyarwar jami’ar jihar Yobe.

Gwamna Buni ya kara da cewa, “Haka kuma muna da wani shirin ci gaba da samar da ingantaccen tsarin karfafa gwiwa tare da ci gaban su da ba su cikakken goyon baya, ta hanyar ba su gidajen da za su zauna hadi da kayan aiki na zamani don su kasance suna tafiya kafada da kafada da zamani a asibitin koyarwar kana da sauran manyan asibitocinmu da ke fadin jihar Yobe”.

Da yake jawabi, kwamishinan ma’aikatar kiwon lafiya a jihar Yobe, Dokta Muhammad Lawan Gana ya bayyana cewa bayan kammala wannan cibiya ta kula da lafiyar kananan yara, hakan zai bai wa asibitin cikakkiyar damar samun rijista da hukumar kula da kwararrun likitocin ta ‘Medical and Dental Council’ hadi da hukumar kula da jami’o’i ta Nijeriya (NUC) da sauran bangarori.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here