Na Yadda Musulunci Addinin Zaman Lafiya Ne – Fasto Suleiman

0
348

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN cocin Omega Power Ministries ta duniya, Fasto Johnson Suleman ya bayyana ra’ayinshi a kan matsalolin da ake samu a fannin addinin Musulunci.

Sanannen abu ne cewa kiristoci da wasu kungiyoyinsu suna kallon addinin Musulunci a matsayin addinin tashin hankali saboda ta’addanci da kungiyoyin ‘yan ta’addan da suke fitowa suke ikirarin cewa addinin suke yi.

Amma kuma wani fasto ya fito kuma ya yi magana ta wani bangare daban. A yayin da ISWAP suka halaka Kiristoci 11 a kwanakin baya, faston ya bayyana cewa Musulunci addini ne na lumana kuma da kanshi ya karanta Qur’ani sama da sau shida. Ya tabbatar da cewa littafin bai taba umartar wani ya kashe mutum dan uwanshi ba.

A kalamanshi: “Qur’ani ya ce duk wanda ya kashe rai daya tamkar ya kashe dukkan mutane ne. ISWAP shaidanu ne kuma Ubangiji zai hukunta su. Kun cire kan Kiristoci 11 ko? A shekarun da suka gabata, na karanta Qur’ani sama da sau shida. Babu musulmi nagari da zai kashe wani mutum. Musulunci addini ne na salama”.

Kungiyar Kiristoci ta kasa da Shugaban kasa Buhari sun kushe kisan da aka yi wa Kiristocin a kwanakin baya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here