A Shirye Muke Don Kai Wa Duk Wata Al’umma ‘Daukin Gaugawa – Hukumar NSCDC

0
388

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

HUKUMAR Jami’an Tsoro na NSCDC wato Civil Defence reshen Jihar Kaduna, ta bayyana cewa a shirye take da ta kai wa kowace al’umma dauki a duk inda suke cikin gaigawa domin a kodayaushe suna zaman shirin ko-ta-kwana ne na ganin cewa sun share wa al’ummar jihar baki daya hawayensu a kodayaushe.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ASC Orndiir Terzungwe ne bayyana hakan a wata zantawarsa da wakilinmu, inda ya bayyana cewa jami’an suna aiki tukuru ba dare ba rana ne domin ganin cewa sun cika wa al’umma bukatunsu muddun aka sanar da su.

Ya kara da cewa dukda yake hukumar tasu ta NSCDC ba ta da ofisoshi a kowane yanki na fadin Jihar, jami’ansu na daya daga cikin jami’an tsaron da ke aiki na Operation Yaki wanda hakan ya kara ba su wata damar da za su iya garzayawa duk wasu wajeje kasantauwar lambarsu na daya daga cikin lambobin da ake kira na jami’an Operation Yaki din.

A cewarsa, dukda yake hukumar ta Civil Defence na dan fama da kalubale na karancin ma’aikata, to amma dukda hakan tana kokarin ganin cewa ta bude wasu kananan ofisoshi a kowane yanki dukda yake suna da manyan ofisoshi a kowace karamar hukuma, wanda a karkashinsu kuma akwai wasu kananan ofisoshi a wadansu wuraren da aka bude a wasu gundumomi.

Ya ce ” kamar misali a garin Rigasa, a halin yanzu muna kokarin bude wani karamin ofishi a tashar jirgin kasa don ganin cewa an kara samun tsaro a wannan yankin saboda irin kalubalen da suke fuskanta na rashin isasshen tsaro, kana da rage matsalar rashin kiranmu ko sanar da mu faruwar al’amura da wasu al’ummar yankin ba sa yi a duk sanda aka samu faruwar wasu abubuwan da ya kamaci a ce mun kai dauki cikin gaugawa, to amma bude ofishin zai kara taimakawa wajen toshe wannan kafar. ”

“Kana ga duk al’ummar da ke da bukatar samun jami’anmu a cikin kowae yankin ko gunduma, suna iya samar mana da wani wuri wanda za mu bude wani karamin ofishinmu da za a iya garzayawa ko zuwa don ganawa da ma’aikatanmu a kan duk wata bukata, domin a shirye hukumarmu take da ta ba da jami’an tsaron da za su yi aiki a wannan wajen kamar yadda muka yi a Unguwar Dosa da wasu wurare da suke da bukatar yin irin hakan.” Inji Shi

ASC Orndiir, ya ci gaba da cewa rashin ganin ofisoshinsu a kusa ba shi ba ne zai sanya al’umma su ki sanar da su faruwar al’amura domin su ma jami’an tsaro ne da ke duk wasu ayyukan da ya shafi tsaro a kasa baki daya, saboda su ma ayyukansu ne aikin da ya shafi kare dukiyoyin da lafiya, kana da raba rikici a cikin al’umma.

A karshe, Jami’in ya yi kira ga al’umma da su garzaya duk wasu ofisoshinsu mafi kusa don bayyana bukatunsu kana su daina yin sakaci na rashin sanar da su faruwar al’amura wanda suke ganin ba dai-dai ba ne ko suke neman a bi musu hakkinsu a kai

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here