MUN KIRA TARON KWAMITIN TUNTUBA NA HARKAR TSARO – INJIYA KUTAMA

0
384

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba

AN bukaci gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Kadimul Islama Dokta Abdullahi Umar Ganduje da kara karfafa harkar tsaro a karamar hukumar Gwarzo duk da kasancewa wanda ake da shi na  bakin kokari wajen gudanar da ayyukansu. Karamar hukumar Gwarzo tayi iyaka da jihar Katsina ta kusurwar yamma yayin da ta kusurowin gabas ,kudu da arewa kuma ta yi da Kabo, Karaye da kuma Shanono.

Injiniya Bashir Abdullahi Kutama shugaban karamar hukumar ne ya bukaci haka lokacin da ya kirawo taron kwamitin da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar ranar Alhamis da ta gabata yayin da sama da mutum dari biyar ne suka halarci taron wanda makasudun kiran taron domin a gano bakin zaren yadda za a kara karfafa matakan tsaro da kuma inganta wadanda ake da su a karamar hukumar da kuma a tattauna yadda za a tunkari matsalolin idan har ma hakan ta taso.

Tun farko a jawabinsa jagoran taron wanda har wayau shi ne shugaban karamar hukumar Injiniya Bashir Abdullahi Kutama ya fara gode wa Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda ya sanya karamar hukumar a zuciyarsa yake biya mata bukatunta kodayaushe ta mika masa bukatar ta musamman yadda ba ya yin kasa a gwiwa kan abin da ya shafi tsaro a wannan karamar hukuma. Injiya Kutama ya jinjina wa Gwamnan bisa yadda harkar tsaro take ba bu wasa a jihar da ma kafa rundunar hadin gwiwa ta tsaro a karamar hukumar wato JTF.

A nasa jawabin yayin gudanar da taron, tsohon mataimakin Gwamnan jihar Kano Abdullahi Tijjani Muhammad wato ATM ya kawo shawarar a kafa kwamitin samar da dabarun tsaro a karamar hukumar.Daga cikin manyan mutane da suka halarci taron sun hada da Abdullahi Tijjami Muhammad tsohon mataimakin Gwamna da Dokta Kabir Getso kwamishinan ma’aikatar muhalli. Sauran su ne Kabiru Ado Lakwaya, kwamishina a ma’aikatar matasa da wasanni, sai Honarabul Haruna Kayu dan majalisar dokokin jiha da kuma babban manajan ma’aikatar gidan ajiye namun daji  Sa’du Ahmad Gwarzo da Hakimin Gwarzo mai girma Kabiru Shehu Bayero.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here