Ta Yaya Ake Neman Kassara Al’amura A Nijeriya – Felix Hassan

  0
  395

  Mustapha Imrana Abdullahi

  SHUGABAN Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kaduna Mista Felix Hassan Hyat ya bayyana wa dimbin ‘ya’yan jam’iyyar a wajen taron da suka kira a babbar hedikwatar jihar cewa ta yaya ‘ya’yansu a yanzu suke tabbatar su ta yaya na daya zai zama na hudu? Kamar yadda ya bayyana cewa da fadin hakan kowa ya san al’amura ba sa tafiya daidai a kasa baki daya.

  Ya yi wa ‘ya’yan jama’ar tuni cewa rashin gaskiya ba zai kai kasar ko ina ba, inda ya ci gaba da ankarar da dimbin jama’ar cewa kowa ya san irin yadda lamari ya faru a zamani marigayi Abacha lokacin yana shugaban kasa yadda wadansu mutane 34 suka yi rayuwar Daka sun yi ban-kwana da iyalinsu domin kawai su ceci Nineriya a wannan lokaci wanda hakan ne ya kawo faruwar Dimokuradiyyar da muke ciki a halin yanzu, amma yanzu sai ga shi ana ta kokarin yin al’amura a karkace.

  “Irin yadda abubuwa ke faruwa a kotuna lamarin babu dadin ji ko kadan domin abubuwa na tafiya a karkace saboda bankarewar lamura a kasar baki daya”.

  Felix Hassan ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su tashi tsaye domin kare kundin tsarin mukin kasa da kuma mutuncin ‘yan Nireriya baki daya. Saboda ana ta yin shari’u tare da yanke hukuncin da ke da alamun tambayoyi a tattare da su.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here