Za A Gina Dakin Rainon Yara A Makarantar Kawo

0
351

Mustapha Imrana Abdullahi

KWAMISHINN kula da ma’aikatar ilimin Jihar Kaduna Dakta Shehu Muhammad ya bayyana cewa za a gina ingantaccen dakin rainon yara a makarantar sakandare ta Kawo cikin garin Kaduna.

Kwamishina Shehu Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da shi da tawagarsa suka kai ziyarar gani da ido yadda harkokin koyarwa da kuma yadda yara dalibai suka dawo makaranta tun bayan dawowa daga hutu a jihar.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa, babban dalilin da ya sa za a gina wannan dakin rainon yara shi ne saboda irin yadda mata malamai suke da yawa da suka kai shittin (60) a wannan makaranta, saboda idan an gina wannan dakin raino zai ba malaman mata damar su gudanar da aikinsu na koyar da dalibai kamar yadda ya dace.

Ya kuma ce za a gina karin Ajujuwa da Ban-dakuna domin zagayawa ga duk masu bukatar yin haka  a makarantar.

Duk da kamar yadda Kwamishinan ilimin ya bayyana cewa dalibai sun dawo a kan kari, ya kuma yi kira ga iyayen yara da su kokarta domin ganin ‘ya’yansu sun dawo makarantar saboda lokacin karatu ba zai jira kowa ba.

Ko a cikin wata sanarwar da ma aikatar ilimin jihar karkashin jagorancin Dakta Shehu Muhammad ta bayyana cewa za a hukunta masu kunnen kashin da suka kasa dawowa makaranta a kan kari.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here