An Rushe Gidan Wani Mai Garkuwa Da Mutane A Katsina

0
787

Mustapha Imrana Abdullahi

GWAMNATIN jihar Katsina tare da hadin gwiwar jami’an tsaron Sojoji da ‘yan sanda sun jagoranci rusa tare da kona gidan wani barawo mai garkuwa da mutane don neman kudin fansa a dajin Gwarjo da ke cikin karamar hukumar Matazu.

A ranar talatar da ta gabata 21/01/2020 Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen karamar hukumar Danmusa suka samu bayanan sirri daga wadanda suka tuba daga sata suka karbi sasanci suka rumgumi zaman lafiya, tare da taimakon su suka kai samame a dajin Gwarjo lokacin da aka kaima Inusa Boka Mai Garkuwa da mutane wanda ya addabi yankin karamar hukumar Matazu da Musawa ya a karbar  kudin fansa.

Bayan dauki ba dadi da yan Sandan suka yi da Mai Garkuwa da mutanen daga Karshe sun samu nasarar kashe shi tare da kubutar da wata mata Mai suna Fiddausi Yusuf da danta mai watanni bakwai mai suna Aminu Yusuf da ya yi Garkuwa da ita ya ajeta a gidan shi.

Gwamnatin jihar Katsina ta ba da umurnin duk wanda aka kama da Garkuwa da mutane a gidan shi za’a rushe gidan kwata-kwata.

A lokacin rusa gidan Inusa Boka Mai Garkuwa da mutane, jami’an tsaron sun gudanar da bincike a gidajen da ke makwabtaka da gidan, inda suka samu bindiga guda biyu kirar hausa mai daukar albarusai na babbar bindiga mai suna AK tare da kwabsar albarusan Babbar bindigar.

Sun kuma samu nasarar kama mutum biyu a gidan wadanda ake zargin sune suka mallaki bindigogin.

A zantawar mu da wani mazaunin kauyen Gwarjo da ke cikin karamar hukumar Matazu, “ya sheda mana cewa sunji dadin wannan nasara da aka samu ta kashe wannan Babban barawo daya addabesu.

“Dama ya matsa ma wannan yanki namu da sace, sacen mutane yana Garkuwa dasu yana neman kudin fansa”. Inji shi”.

Ya ci gaba da cewa da yaddar Allah yankin za’a samu saukin satar mutane da ake ana neman kudin fansa”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here