Sojoji Sun Buɗe Wuta A Kan ‘Yan Sandan Da Suka Fatattaki Boko Haram

0
1027

Rabo Haladu Daga Kaduna

AN shiga rudani a garin Mainok, da ke babban hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a jihar Borno, bayan wasu Sojoji sun bude wa jami’an ‘yan sandan SARS da suka yi artabu da  ‘yan Boko Haram.

Cewar TheCable Ofishin SARS sashe ne na hukumar ‘yan sandan Najeriya da suka shahara da yakan ‘yan fashi da makami.

Kauyukan da ke tsakanin Borno da Yobe na fuskantar barazana daga hannun ‘yan Boko Haram tun da aka shiga sabuwar shekara.

A ranar Litnin da suka sake kawo hari Mainok, an ce Sojoji da ‘yan garin sun arce, hakan ya bai wa ‘yan ta’addan daman cin karansu ba babbaka.

Amma jami’an ‘yan sandan SARS da RRS suka dumfari ‘yan ta’addan kuma suka kawar da su, cewar wani mazaunin Mainok.

Daya daga cikin jami’an SARS din da suka fatattaki ‘yan Boko Haram ya bayyanawa manema labarai cewa bayan dakile ‘yan ta’addan kuma suna kokarin fitowa, sai Sojoji suka bude musu wuta.

Jami’in dan sandan wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya ce abin ya ba su mamaki da suka ga Sojoji ke harbinsu. Ya ce: “An tura mu Mainok bayan samun labarin cewa ‘yan Boko Haram sun kai hari. Da muka isa wajen, mun tarar yan Boko Haram sun kashe mutane kuma sun lalata gidajensu.”

“Sai muka bude musu wuta na tsawon kimanin awa daya. Mun samu galaba a kansu kuma mun kwace motocinsu biyu Hilux da makamai.

Abin mamakin shi ne yayin da muke kokarin fitowa, wasu Sojoji suka kawo mana hari.” “Sun har-harba mana rokoki har daya daga cikin motoci maras jin bindiga da sifeto janar ya ba mu ya lalace.”

Ya ce amma kwamandansu ya umurce su kada su harbi Sojojin har sai lokacin da wasu Sojoji suka zo daga Benisheik suka tsagaita wuta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here