Ebola ya kashe Bahagon ‘Yan Sanda a Marabar Nyanya

  0
  638

   Daga  Z A Sada

  SHAHARARREN dan damben gargajiyar Hausawa, Abdurrazak Ebola ya yi nasarar doke Bahagon Shagon ‘Yan Sanda a damben mota da suka yi a marabar Nyanya ranar Lahadi.

  Damben na gasar mota na jihar Kaduna ne, amma Umar Fillo shugaban kungiyar damben Kaduna ya kai wasan Marabar Nyanya da ke jihar Nasarawa, Najeriya.

  Tun da fari sai da aka bar matasa da manyan ‘yan dambe suka fafata a tsakaninsu kafin wasan Ebola da Bahago. Cikin wasannin da aka yi har da canjaras tsakanin Kurman Guramada da Bahagon Musan Kaduna daga Arewa.

  Sai Garkuwan Bahagon Shagon ‘Yan sanda daga Jamus ya doke Autan Dan Gero Guramada.

  Sai da agogon ya kai sha biyu saura, sannan ne Umar Fillo ya shiga fili ya zayyana dokokin damben tare da Idris Bambarewa shugaban damben jihar Nasarawa.

  Daga nan ne Alkalin wasa, Shagon Amadi ya daure hannun Ebola da Selotif da kuma na Bahagon ‘Yan sanda.

  Daga nan ne aka hura wasa suka fara dambe a tsakaninsu, inda suka yi minti uku turmin farko babu kisa aka raba.

  Bayan da suka sha ruwa aka koma turmi na biyu ne Abdurrazak ya yi nasara a kan Bahagon Shagon ‘Yan sanda.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here