Jihar Zamfara Na Da ‘Ya’yan Bedin Da Ya Fi Na Kowace Jiha Kyau – Zailani Baffa

0
609
Mustapha Imrana Abdullahi
AN bayyana jihar Zamfara a matsayin jihar da ke da ‘ya’yan Bedin da ya fi na kowace jihar kyau a fadin Nijeriya.
Zailani Baffa mai taimaka wa Gwamnan Jihar Zamfara a kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta Liberty a Kaduna
Zailani Baffa ya ce wannan arziki na ‘ya’yan Bedi kamfanoni da yawa na bukatar shi domin sarrafawa a yi abubuwa da dama na inganta rayuwar jama’a. Ya kuma ci gaba da cewa kamfanonin sarrafa ma’adinai da dama ne da ke kasar Sin wato Chaina suka gayyaci Gwamnan Zamfara Alhaji Mihammadu Bello Matawallen Maradun saboda zaman lafiya da aka samu a jihar.
“Akwai ma’adinai guda 17 a dankare a cikin jihar Zamfara cikinsu har da Gwal kuma kamfanonin suna bukatar su domin amfaninsu da jiharmu baki daya.
Ana nan za a samar da wata ma’aikatar da za ta yi aiki a kan kiyaye hakkin dukkan mai hakki idan wani kamfanin ma’adanai na bukatar hakowa da sarrafa ma’adanin jihar Zamfara, tun daga kan karamar hukuma zuwa jama’ar da ke cikin ta baki daya.
“Akwai wata kasuwa a kasar Dubai da na gani a tashar Talbijin ta channels da ake cewa kasuwar Zamfara Gwal, kawai ana sayar da Gwal na Jihar Zamfara haka kawai ba tsari, shi ya sa yanzu Gwamnan Zamfara ya samar da ingantattun tsare tsaren da kowane dan jihar Zamfara zai amfana da arzikin da Allah ya hore wa jihar”, inji Zailani Baffa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here