Gwamna Lalong Ya Yi Umurnin Kama Shugabannin Wasu Garuruwa Cikin Gaggawa

0
355

Daga Usman Nasidi.

GWAMNAN jihar Filato kuma shugaban gwamnonin Arewa, Simon Lalong a ranar Talata, 28 ga watan Janairu ya yi umurnin dukkanin shugabannin Fulani a kananan hukumomin Bokkos, Mangu, Riyom da Barkin Ladi da ke jihar yayin da yawan mutanen da suka mutu a harin karshen mako ya tasar wa 22.

Lalong ya bayar da umurnin ne ga kwamishinan ‘yan sanda, Isaac Akinmoyede a lokacin wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki, shugabannin Fulani da shugabannin garuruwa da na addini wanda ya gudana a gidan gwamnati a Jos.

Gwamnan wanda ya fusata da nuna bakin ciki a kan ci gaba da kai hare-haren da kashe-kashe da ‘yan bindiga ke kai wa wasu kauyuka a Bokkos da Mangu, ya ce ba zai sake lamuntar haka ba.

“Ina magana ne a madadin jihar Filato a matsayin shugaban tsaro, tun da ba a kama kowane mai laifi ba kuma har yanzu ana kashe mutane; a kama dukkanin Ardon Fulani da shugabannin garuruwan har sai an fito da wadanda suka aikata laifin.

“Ba ma tsoron wadannan ‘yan ta’addan, babu wanda ya fi karfin gwamnati! Ta yaya za ku fada mani cewa ba a kama kowa ba, shin aljanu ne masu kisan? Allah zai tona masu asiri kuma ba zan sake lamunta ba a jihar Filato ya isa haka!”

Lalong wanda ya nuna bakin ciki da bacin rai a kan kashe-kashen, ya yi umurnin gaggawar kama shugabannin Fulani da na garuruwan da suka halarci taron, sannan cewa a tsare su a hannun ‘yan sanda har sai an fito da masu laifin.

Kwamishinan ‘yan sandan ma ya nuna bakin ciki kan cewa wasu shugabanni na boye masu laifi a garuruwansu wadanda ke kaddamar da hare-hare da kashe-kashe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here