Sun Kai Hari Rugar Fulani, Sun Kona Gidaje 23 Da Masallaci

0
345

Daga Usman Nasidi.

A wani lamari mai kama da ramuwar gayya biyo bayan kisan wasu mutane 13 a kauyen Kwatas da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Filato, wasu fusatattun matasa sun kai hari Rugar makiyaya, inda suka cinna wa gidaje 23 da wani masallaci wuta a yankin.

Da suke jawabi ga manema labarai a ranar Talata, 28 ga watan Janairu, kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) da rakwarata ta GAN Allah, sun tabbatar da harin, inda suka bayyana lamarin a matsayin abin Allah wadai da rashin Imani.

Yayin da suke Allah wadai da harin baya da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13, kungiyoyin sun bayyana yadda aka rataya lamarin a wuyan makiyaya a yankin a matsayin abin kaico.

A cewarsu, bai kamata a yanke hukuncin cewa makiyaya ne suka yi harin ba domin babu hujjar da ke tabbatar da hakan.

Yayin da yake kira ga gwamnati da hukumomin tsaro a kan su yi bincike da tsamo masu laifin ko su fuskanci doka, Mista Bappa ya bukaci dukkanin mutanen jihar da su kwantar da hankalinsu sannan su rungumi zaman lafiya.

A halin da ake ciki, Gwamnan jihar Filato kuma shugaban gwamnonin Arewa, Simon Lalong a ranar Talata, 28 ga watan Janairu ya yi umurnin dukkanin shugabannin Fulani a kananan hukumomin Bokkos, Mangu, Riyom da Barkin Ladi da ke jihar yayinda yawan mutanen da suka mutu a harin karshen mako ya tasar na 22.

Lalong ya bayar da umurnin ne ga kwamishinan yan sanda, Isaac Akinmoyede a lokacin wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki, shugabannin Fulani da shugabannin garuruwa da na addini wanda ya gudana a gidan gwamnati a Jos.

Gwamnan wanda ya fusata da nuna bakin ciki a kan cigaba da kai hare-haren da kashe-kashe da yan bindiga ke kai wa wasu kauyuka a Bokkos da Mangu, ya ce ba zai sake lamuntan haka ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here